27 Afirilu 2021 - 12:40
Chadi : An Nada Wanda Idriss Deby Ya Kora Firaministan Wucin Gadi

Majalisar sojojin dake rike da mulki a kasar Chadi, ta nada Albert Pahimi Padacké, a matsayin firaministan gwamnatin wucin gadi.

ABNA24 : Mista Padacké, wanda sananen dan siyasa ne a kasar, shi ne firaminista na karshe a kasar kafin a soke mukamin a watan Mayun 2018, lokacin da aka kwaskware kundin tsarin mulkin kasar.

Kuma shi ne wanda ya zo na biyu a zaben shugabancin kasar da ya gabata na ranar 11 ga watan Afrilu 2021, wanda tsohon shugaban kasar mirigayi Idriss Deby Itno, ya lashe.

Masana da dama dai na ganin nadin da majalisar sojojin kasar ta yi, abun a yaba ne, kasancewarsa wanda ya san siyasar kasar kuma yana da hulda da kungiyoyin fara hula da dama a kasar.

Saidai kuma wasu sun soki nadin da akayi masa kasancewar ya taba zama firaministan Deby, yanzu kuma bai kamata ya kasance firaministan dan Idriss Deby ba.

Tuni dai jam’iyyun adawa na kasar suka kudiri anniyar fitowa kan tituna domin bukatar ganin an dama da kowa a siyasar kasar da kuma mika mulki ga fafar hula.

342/